Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya baiwa Kwamitin haɗin gwiwa kan yaƙi da shan miyagun kwayoyi da faɗan daba cikakken ‘yancin gudanar da ayyukansa, bayan ya sanya hannu kan dokoki guda biyu da ke ƙarfafa yaƙi da matsalolin biyu a faɗin jihar.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da yake ƙaddamar da kwamitin, inda ya ce shan miyagun ƙwayoyi na daga cikin manyan matsalolin da ke addabar Kano.
A cewar sa duk da kusan kashi 60 cikin 100 na al’ummar jihar matasa ne, abin takaici ne yadda Kanon ke cikin jihohin da matsalar shaye-shayen miyagun ƙwayoyi ta fi kamari, tare da tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta samarwa da kwamitin isassun kuɗaɗe, tsaro, ofisoshi, motocin aiki da sauran kayan aikin da za su taimaka wajen yaƙi da matsalar.
Gwamna Abba ya ce shaye-shayen miyagun ƙwayoyi na matukar lalata rayuwar matasa, da hana su ci gaba da karatu, tare da haifar da aikata laifuffuka da raunana zaman lafiya, haka kuma yana haddasa asarar tattalin arziki sakamakon rage yawan masu aiki da kuma ƙarin kuɗaɗen da ake kashewa wajen yaƙi da laifuffuka.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Gwamnan na cewa shan miyagun ƙwayoyi na da alaƙa da ayyukan ‘yan daba, waɗanda ke haddasa rikice-rikice, tsoratar da jama’a, kwacen wayoyi da sauran miyagun laifuffuka, inda ya ce gwamnati za ta ci gaba da faɗaɗa cibiyoyin gyaran halin masu shaye-shaye, wanda a halin yanzu Kano take da cibiyoyi 2 a Ƙiru domin maza da kuma Gaya domin mata.
