Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta sanya ranar 14 ga Afrilu domin sauraron shari’ar da ke kalubalantar shugabancin jam’iyyar ADC na kasa karkashin jagorancin tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata David Mark.
Mai ƙarar, Nafiu Bala Gombe, na neman kotu ta hana David Mark da wasu shugabannin jam’iyyar bayyana kansu a matsayin halastattun shugabanni.
Kotun ta ɗauki wannan mataki ne bayan umarnin Kotun daukaka ƙara da ya bukaci a ci gaba da shari’ar.
A halin yanzu, ɓangaren Sanat David Mark ya nemi kotu ta umarci hukumar INEC ta mayar da sunayensu a tsarin rajista, yayin da su kuma suka bukaci a yi watsi da ƙarar, suna mai cewa ba ta da tushe kuma kotu ba ta da hurumin sauraron lamarin.
