Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sayi fom din nuna sha’awar tsayawa takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC a shekarar 2027 domin neman wa’adi na biyu.
Rahotanni sun ce dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Ikeja ta jihar Legas James Faleke ne ya karbi fom din a madadin Shugaba Bola Tinubu, a wani biki da aka gudanar a Talatar a birnin tarayyar Abuja, inda Sakataren Tsare-tsare na Kasa na jami’iyyar APC Suleiman Argungu, ya mika takardun bayan bude shirin sayar da fom din.
James Faleke, wanda ke jagorantar kungiyoyin magoya bayan Tinubu, ya biya kudin fom din da ya kai naira miliyan 100, lamarin da ke nuna fara shirin yakin neman zaben shugaban kasar a cikin jam’iyya mai mulki.
Hukumar zabe ta kasa INEC, ta sanya ranar 16 ga Janairun 2027 domin gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun dattawa da kuma na wakilai.
Sai kuma ranar 6 ga Fabrairun 2027 wanda za a gudunar da zaban gwamnoni da kuma yan majalisun jihohi.
Hukumar ta ce za a gudanar da zabukan fidda gwani daga ranar 23 ga Afrilu zuwa 30 ga Mayun 2026, sannan yakin neman zabe zai fara daga watan Agusta zuwa Satumba na shekarar 2026.
