Gwamnatin jihar Kano ta sanar da shirin raba bishiyoyi guda miliyan 10 a wannan shekara domin samar da muhalli mai lafiya da tsafta.
Kwamishinan Muhalli da Sauyin Yanayi, Dakta Dahir Muhammad Hashim ne ya bayyana hakan yayin wata ziyarar gani-da-ido da ya kai wuraren rainon bishiyoyi a ƙananan hukumomin Gwarzo da Dawakin Kudu.
A cewarsa, bishiyoyin da za a raba sun haɗa da zogale, ɗorawa, lemon tsami, malmo, mangwaro, lemon zaƙi da goba, waɗanda aka shirya rabawa domin al’umma su dasa a muhallansu.
Hashim ya kuma yi kira ga ƙungiyoyin al’umma da makarantu da su nemi wannan dama ta hanyar cike fom ko tuntubar ma’aikatar domin samun bishiyoyin da za su dasa a yankunansu.
Gwamnatin ta jaddada cewa wannan shiri na daga cikin matakan da take ɗauka na inganta rayuwar al’umma da kare muhalli a fadin jihar.
