Tsohon Gwamnan Jihar Sokoto, Sanata Aminu Waziri Tambuwal, ya buƙaci hukumomin tsaro su gudanar da bincike kan zargin kai hari ga ɗan takarar gwamnan jihar na jam’iyyar ADC, Manir Muhammad Dan’iya, tare da tawagarsa.
Tambuwal ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar Juma’a, 30 ga Oktoba, 2026, a kusa da filin jirgin saman Sokoto.
A cewarsa, wasu jami’an tsaron jihar sun tare ayarin motocin ɗan takarar, inda ya yi zargin cewa an harba bindigogi tare da lalata motarsa.
Tsohon gwamnan ya kuma yi zargin cewa an tsare jami’an Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) guda biyu da ke cikin tawagar tsaron ɗan takarar.
Tambuwal ya buƙaci rundunar ƴan sanda da sauran hukumomin tsaro su gudanar da cikakken bincike kan lamarin, tare da ɗaukar matakin da doka ta tanada kan duk wanda aka samu da hannu.
Ya kuma yi kira ga magoya bayan jam’iyyar ADC da su kwantar da hankalinsu, su guji duk wani mataki da ka iya haddasa tashin hankali.
A cewarsa, zargin harin ba zai hana jam’iyyar ADC gudanar da taron ƙaddamar da yaƙin neman zaɓenta na shugaban ƙasa da aka shirya yi a ranar 4 ga Nuwamba, 2026, ba.
