Rundunar ’Yan Sandan Jihar Borno ta ce mayaƙan da ake zargin na ƙungiyar ISWAP ne suka yi awon gaba da duk ɗaliban da ke cikin ajujuwa lokacin da suka kai hari a Makarantar Sakandaren Gwamnati ta Lassa da ke ƙaramar hukumar Askira-Uba a ranar Litinin.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, Nahum Kenneth Daso, ya shaida wa Daily Trust cewa maharan sun kutsa cikin garin Lassa ne a kan babura, suna amfani da damar ranar kasuwa kafin su nufi makarantar.
A cewarsa, maharan sun kashe malami guda tare da yin garkuwa da duk ɗaliban da ke cikin ajujuwa.
Ya ƙara da cewa jami’an tsaro sun yi artabu da maharan, lamarin da ya rage yawan mutanen da suka yi garkuwa da su.
Majiyoyin yankin sun ce maharan sun mamaye makarantar da misalin ƙarfe tara na safe, inda suka riƙa harbe-harbe kafin su shiga ɗakin jarabawa, lokacin da ɗaliban aji na ƙarshe ke rubuta jarabawar NECO. Daga nan ne suka yi awon gaba da wasu ɗalibai da malamai zuwa wani wuri da ba a sani ba.
Kakakin ’yan sandan ya ce jami’an tsaro na ci gaba da sintirin dazukan da ke kewaye da yankin domin ceto waɗanda aka sace.
Wannan hari ya zo ne kwanaki 47 bayan sace ɗalibai 42 na Mussa Primary da Junior Secondary School a wannan ƙaramar hukuma ta Askira-Uba.
A ranar Lahadi, iyayen waɗannan ɗaliban sun bayyana damuwarsu, suna mai cewa har yanzu masu garkuwar ba su tuntube su ba, lamarin da ya ƙara tayar musu da hankali kan makomar ’ya’yansu.
