Wata kotu a Mali ta yankewa wani jami’i a ofishin jakadancin Faransa mai suna Yann V hukuncin zaman gidan yari na shekaru 20 kan zargin yin leƙen asiri da zagon ƙasa ga tsaron ƙasa.
Rahotanni sun ce ana tsare tare da bincike akan wanda ake zargin tun lokacin da aka kama shi a watan Agustan 2025 tare da wasu jami’an Mali da ake zargin suna shirya juyin mulki a ƙasar, inda sai a makon nan ne aka ci tarar sa dalar Amurka 6,225 tare da hana shi shigowa Mali na tsawon shekaru 20.
A lokacin da aka kama shi, hukumomin Mali sun zargi jami’in, da aiki ga hukumomin leƙen asirin Faransa, sannan hukumomin na Mali sun soki ƙasashen waje da ke ƙoƙarin kawo rashin kwanciyar hankali a ƙasar.
Sai dai kasar Faransa ta sake jaddada cewa tuhumar da ake yiwa jami’in na ta, wanda yake aiki a ofishin jakadancin Faransa a babban birnin Bamako, ba ta da tushe.
