Shugabannin Fulani a Kano sun yabawa gwamnatin jihar kan matakin da ta dauka na kwato filayen kiwo guda 371 da aka mamaye, da hanyoyin shanu (Burtali/Labi), da sauran albarkatun kiwo a fadin jihar.
Shugaban kungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN) reshen Kano, Kyaftin Abdullahi Bakoji mai ritaya, da takwaransa na kungiyar Fulani Development Association of Nigeria (FULDAN), Alhaji Sani Adamu, ne suka bayyana hakan a wata tattaunawa daban-daban da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya.
Kyaftin Bakoji ya bayyana matakin a matsayin abin a yaba kuma wani shiri ne mai kyau na kare filayen kiwo da hanyoyin shanu domin tabbatar da zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin makiyaya da manoma.
A nasa bangaren, Shugaban FULDAN na Kano, Alhaji Sani Adamu, ya bukaci Ma’aikatar Kula da bunkasa kiwon Dabbobi ta jihar da ta tabbatar da aiwatar da mataki yadda ya kamata, yana mai cewa hakan zai hana manoman da suka saba karya doka komawa wuraren da aka kwato.
Ya bayyana fatan cewa matakin zai taimaka wajen kare hakkokin makiyaya da kuma tabbatar da zaman lafiya mai dorewa tsakanin al’ummomin jihar.
