Shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin Kano Hon. Lawan Hussaini ya nuna takaicinsa akan kalaman malamin addinin nan da ya jinginawa Ma’aiki Sallahu AlaiHi Wa Sallam kwarkwata, yana mai cewa babu babban rashin ladabi da tarbiyya saman hakan.
Lawan Hussaini, wanda ke wakiltar Dala a majalisar ya ce dole ne al’umar Kano su farka su yaƙi duk wasu ta’adodi da ke lalata tarbiyyarsu da managartan al’adun da aka sansu akai tun fil azal.
Mamban ya furta hakan ne a tattaunawarshi da shirin Rigar ƙaya na Lumana Radio, yayin da yake ƙoƙarin kare matakin da majalisar ta su ta ɗauka akan dakatar da wani mambansu saboda zargin rashin ladabi, yana mai cewa dandulan zamani na neman zamewa al’uma matsala wajen furta
kalaman rashin tarbiyya da ladabi ga masu daraja, mafi muna yace ace ana jinginawa Manzon tsira kalmomi kamar na ƙwarƙwata da sunkai matuƙar saɓo da munin ladabi.
