Lauyoyi Sun Nemi Majalisar Kano Ta Binciki Hayar Shagunan Masallaci
Lauyoyi Sun Nemi Majalisar Kano Ta Binciki Zargin Karkatar da Naira Miliyan 9 a Kano
Lauyoyin Kabiru S. Saleh da Mahmud I. Khalil ne suka shigar da ƙorafin a gaban Majalisar Dokokin Jihar Kano, kan zargin almundahana da karkatar da kuɗaɗen hayar shaguna 54 mallakin Masallacin Juma’a na Sheikh Tijjani Usman Langon Bare-Bari, da ke yankin Kurna Asabe, a Ƙaramar Hukumar Dala.
A cikin ƙorafin, lauyoyin sun bayyana cewa Alhaji Ibrahim Namadi, wanda ke da alhakin karɓa da kula da kuɗaɗen hayar shagunan, ya tattara kuɗaɗen da suka haura Naira miliyan tara tsakanin shekarar 2024 zuwa 2025.
Sun yi zargin cewa duk da buƙatun da wasu daga cikin al’ummar masallacin suka sha yi, Alhaji Ibrahim Namadi ya gaza gabatar musu da cikakken bayani kan adadin kuɗaɗen da aka tara, yadda aka kashe su da kuma ayyukan da aka gudanar da su.
Lauyoyin sun ƙara da cewa rashin samun bayanan kuɗaɗen shiga da kashewa ya haifar da damuwa da rashin yarda tsakanin al’ummar masallacin, musamman bisa zargin yiwuwar karkatar da wani ɓangare na kuɗaɗen.
A ƙorafin da aka miƙa wa Kakakin Majalisar a ranar 22 ga Mayun 2026, lauyoyin sun buƙaci Majalisar ta gudanar da cikakken bincike, tare da gayyatar Alhaji Ibrahim Namadi da sauran waɗanda abin ya shafa domin amsa tambayoyi da gabatar da bayanan kuɗaɗen.
Sun kuma buƙaci a ɗauki matakin doka da gudanarwa idan bincike ya tabbatar da almundahana, karkatar da kuɗaɗe ko karya amana, tare da tabbatar da dawo da duk wani kuɗi da aka samu an karkatar da shi ba bisa ƙa’ida ba.
Sai dai zarge-zargen da ke cikin ƙorafin ba su zama tabbataccen laifi ba, domin ana buƙatar gudanar da bincike da kuma bai wa wanda ake zargi damar mayar da martani.
