Sarkin Katsina, Abdulmumini Kabir Usman, ya bukaci jam’iyyar APC da shugabanninta da su daina yaudarar yan Najeriya game da halin da kasar ke ciki, yana mai cewa rashin tsaro na hana manoma zuwa gonakinsu, yayin da matsin tattalin arziki ke kara tsananta.
Sarkin ya bayyana hakan ne lokacin da Sanata Abdulaziz Abubakar Yari, Darakta-Janar na kwamitin yakin neman zaben shugaba Tinubu na shekarar 2027, ya kai masa ziyara a fadarsa da ke jihar Katsina.
