Saurari premier Radio
24.5 C
Kano
Sunday, September 8, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiShugaban Amurka Joe Biden ya aike da gayyata ga shugaban Najeriya Bola...

Shugaban Amurka Joe Biden ya aike da gayyata ga shugaban Najeriya Bola Tinubu domin gudanar da wata tattaunawa tsakaninsu.

Date:

Shugaban Amurka Joe Biden ya aike da gayyata ga shugaban Najeriya Bola Tinubu domin gudanar da wata tattaunawa tsakaninsu.
Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Najeriya, Ajuri Ngelale, ya fitar ya ce jakadan shugaban Amurka na musamman, kuma mataimakin sakataren harkokin wajen ƙasar, Ambasada Molly Phee, ne ya bayyana haka lokacin da ya ziyarci shugaba Tinubu a fadarsa.
Mista Phee ya shaidawa Tinubu cewa shugaban Amurka Joe Biden na buƙatar ganawa ta musamman da shi, a lokacin babban taron Majalisar Dinkin Duniya da za a gudanar a birnin New York cikin watan Satumba.
Jakadan na Amurka ya ce Tinubu ne kaÉ—ai shugaban Afirka da shugaban Amurka ya karrama da gayyatar ganawa da shi.
Ya Ć™ara da cewa sun san akwai hanyoyin da zasu bi domin Ć™arfafa zuba jarin Amurka a Najeriya, kuma suna son yin aiki kafaÉ—a-da-Ć™afaÉ—a da Tinubu domin cimma hakan, a wani É“angare na inganta tattalin arzikin Najeriya da ma na Afirka”.
Ya kara da cewa suna yabawa da irin ƙoƙarin da Tinubu keyi wajen samar da yanayi mai kyau ga masu zuba jari.

Latest stories

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muƙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...

Related stories

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muƙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...