Mai Martaba Sarkin Kano, Khalifa Muhammadu Sanusi II, ya halarci taron World Food Congress 2026 da aka gudanar a birnin Hong Kong, domin taya Farfesa Hafiz Abubakar murnar samun karramawa a taron na ƙasa da ƙasa.
Farfesa Hafiz Abubakar, wanda malami ne kuma mamba a kwamitin gudanarwa na Ƙungiyar Masana Abinci da Gina Jiki ta Najeriya (Nutrition Society of Nigeria), ya samu karramawar ne bisa gudummawar da yake bayarwa a fannonin ilimi, abinci da gina jiki.
Taron ya samu halartar masana da ƙwararru daga sassa daban-daban na duniya, inda aka gudanar da tattaunawar kimiyya, jawabai na musamman, baje kolin sabbin fasahohi da musayar ƙwarewa kan harkokin abinci da gina jiki.
Haka kuma, an gudanar da zaman tattaunawa tsakanin masana da liyafar cin abinci ta musamman a matsayin wani ɓangare na taron.
Daga cikin sauran manyan baƙin da suka halarci taron akwai Shugabar Jami’ar Northwest Kano, Farfesa Amina Salihi Bayero, da Magatakardar jami’ar, Dakta Isyaku Adamu.
Karramawar da Farfesa Hafiz Abubakar ya samu na daga cikin abubuwan da suka ja hankali a taron, musamman ganin irin gudummawar da yake bayarwa wajen bunƙasa ilimi da harkokin abinci da gina jiki a Najeriya.
