Hukumar Kula da Cututtuka Masu Yaɗuwa ta Najeriya (NCDC) ta amince da biyan Naira dubu 100 a kowanne mako ga mutanen da ke buƙatar tallafin kuɗi yayin da ake killace su ko sanya su ƙarƙashin sa ido sakamakon yiwuwar mu’amalarsu da mai cutar Ebola a Abuja.
Babban Daraktan hukumar, Dr. Jide Idris, ya ce an ɗauki matakin ne domin taimaka wa waɗanda abin ya shafa wajen biyan kuɗin abinci, masauki da kula da iyalansu yayin da suke bin ƙa’idojin lafiya.
A ranar 25 ga Oktoba, 2026, Najeriya ta tabbatar da mutum ɗaya da ya kamu da Ebola, yayin da aka gano mutane 53 da suka yi mu’amala da shi, waɗanda ake sa ido kan lafiyarsu.
NCDC ta kuma jaddada muhimmancin sa ido na tsawon kwanaki 21 da kuma shirya jihohi wajen tunkarar duk wata annoba.
