Saurari premier Radio
29.9 C
Kano
Saturday, June 15, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiSarkin Kano Muhammad Sunusi II ya shiga fadar masarautar Kano

Sarkin Kano Muhammad Sunusi II ya shiga fadar masarautar Kano

Date:

Sarkin Kano Muhammad Sunusi II ya shiga fadar masarautar Kano.

Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf da mataimakinsa Comrade Aminu Abdulsalam Gwarzo da manyan mukarraban gwamnatin ne suka yiwa sarkin rakiya zuwa gidan Dabo.

Da fari dai an yi ta yada wata sanarwar a shafukan sada zumuta a daren nan dake cewa Sarki Aminu Ado Bayero yana hanyar shiga gidan bisa la’akari da odar dia kotu ta bayar na dakatar da rushe masarautun.

Sai dai daga bisani kwatsam wasu hotuna da Bidiyo sun nuna yadda mukarraban gwamnatin Kano suka yiwa Sarki Muhammadu Sunusi II rikiya zuwa fadar masarautar Dabo a tsakar daren juma’ar nan.

Idan za’a iya tunawa dai a ranar Alhamis ne Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya baiwa sarakunan da ya rushe wa’adin awanni 48 su mayar da dukkanin kayayyakin gwamnati, yayin da yake sanya hannu kan rushe sabbin masarautun da gwamnatin tsohon gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta kirkira.

Latest stories

Related stories