Saurari premier Radio
29.9 C
Kano
Saturday, June 15, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiNuhu Ribadu ya musanta zargin da Mataimakin Gwamna yai masa

Nuhu Ribadu ya musanta zargin da Mataimakin Gwamna yai masa

Date:

Nuhu Ribadu ya musanta zargin da Mataimakin Gwamna yai masa.

Ofishin mai bawa shugaban kasa kan harkokin tsaro, NSA ya musanta zargin da gwamnatin Kano ta yi masa na bayar da jami’an tsaro su dawo da sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero jihar.

Mataimakin gwamnan jihar nan, kwamared Aminu AbdulSalam Gwarzo ya zargi Nuhu Ribadu da bayar da jirage biyu su rako Sarki Aminu Kano.

Kakakin ofishin NSA, Zakari Mijinyawa ya musanta zargin.

Ya shawarci ‘yan siyasa su daina kalaman da ka iya kawo nakasu ga kokarin jami’an tsaro na tabbatar da zaman lafiya a kasar nan.

Latest stories

Related stories