Saurari premier Radio
29.9 C
Kano
Saturday, June 15, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yunkurin kawo cikas ga zaman lafiyan...

Atiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yunkurin kawo cikas ga zaman lafiyan Kano kan batun masarautu

Date:

Atiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yunkurin kawo cikas ga zaman lafiyan Kano kan batun masarautu.

A sanarwar da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Atiku Abubakar ya ce matakin da gwamnatin tarayya ta ɗauka na baza jami’an soji a Kano ya saba da kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 da aka yiwa gyara.

Atiku ya ce matakin rushe masarautun Kano da kuma sake naɗa Muhammadu Sunusi II da gwamna Abba Kabir Yusuf yayi yana kan tsarin doka.

Ya kuma tunatar da gwamnatin shugaban ƙasa Bola Tunubu cewa jihar Kano tana cikin zaman lafiya, don haka duk wani yunkuri na rikita zaman lafiyar jihar ba abune da za’a lamunta ba.

Atiku Abubakar ya ƙara da cewa, a lokacin da aka tsige Muhammadu Sunusi II, ranar 9 ga watan Maris 2020 jihar ta ci gaba da zama lafiya ba tare da wani hargitsi ba.

Latest stories

Related stories