Ba mu ji haushi ba, kuma mun karbi kaddara game da masarautar mu da aka rushe
Sarkin Gaya Alhaji Aliyu Ibrahim Abdulkadir daya cikin masarautu biyar da gwamnatin jihar Kano ta rushe, ya ce sun karbi wannan al’amari hannu-bibiyu a matsayin wata kaddara daga Allah.
Ya bayyana haka ne a ganawarsa da BBC inda ya ce haka Allah ya nufa, don haka ba su ji haushin kowa ba.
’Mu masu karbar kaddara ne, haka Allah ya so kuma haka za a yi dole, ba mu da niyyar mu je wajen shari’a, mun karbi kaddara, mun gode wa Allah’’. A cewar Sarkin Gaya Alhaji Aliyu Ibrahim
BBC Hausa