33.9 C
Kano
Sunday, June 4, 2023
HomeAl'aduSallar Gani: Birnin Gumel yayi cikar Kwari

Sallar Gani: Birnin Gumel yayi cikar Kwari

Date:

Related stories

Maniyyata 17,000 ne suka bar Najeriya zuwa kasa maitsarki-NAHCON

Bayan kwashe kwanaki bakwai da fara jigilar alhazan Najeriya...

Dubban mutane ne suka mamaye birnin Gumel da ke jihar Jigawa domin shaida bikin Sallar Gani na bana.

 

Tuni dai harkokin kasuwanci suka bude a birnin, yayin da samari da Yan manta Suka caba kwalliya domin nuna murna.

 

A bangare guda kuma dalibai ne Yan makaranta ke jerijin gwano suna koma rera wakokin yabon annabi domin nuna murnar zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammad SAW.

 

Tuni dai masu wasannin al’ada Suka fara ajiye kayayyakin su domin baje kolinsu a kofar fadar ta Gumel.

 

Ana sa ran manyan mutane daga sassan kasar nan ne za su halarci bikin na bana.

Tun a jiya Juma’a ne aka fara bikin na bana da addu’o’i a dukkan masallatan Juma’a na Birnin.

 

Sai kuma Hawan Sallar da za a gudanar a yau Asabar da gobe Lahadi baya ga wasannin Al’adun gargajiya da za a gudanar

Latest stories