Sakataren Rundunar Sojin Kasan Amurka, Dan Driscoll, ya mika takardar murabus dinsa ga Shugaban Amurka Donald Trump, bayan rahotannin samun sabani tsakaninsa da Sakataren Yaki Pete Hegseth kan yadda ya kamata a tafiyar da rundunar.
Jaridar Wall Street Journal ta ruwaito cewa murabus din Driscoll ya biyo bayan watanni na rashin jituwa da Hegseth, musamman kan sauye-sauyen shugabancin rundunar da kuma cire wasu manyan jami’an soja daga mukamansu.
Murabus din ya bar Rundunar Sojin Kasa ta Amurka ba tare da wani shugaba a siyasance ba da Majalisar Dattawan kasar ta nada.
A halin yanzu, Janar Christopher LaNeve ne ke rike da mukamin shugaban ma’aikatan rundunar a matsayin mukaddashi.
LaNeve ya karbi mukamin ne bayan Hegseth ya cire magabacinsa, Janar Randy George, daga mukamin a watan Afrilun da ya gabata.
Rahoton ya ce ficewar Driscoll na zuwa ne yayin da ake samun sauye-sauye masu yawa a manyan mukaman soji karkashin jagorancin Hegseth.
Wadannan sauye-sauye sun rage yawan manyan janar-janar masu taurari hudu a rundunar daga 10 zuwa biyar kacal, adadin da rahoton ya ce shi ne mafi karanci cikin shekaru da dama.
Sabon sauyin shugabancin ya biyo bayan tilasta wa Janar Chris Donahue, tsohon kwamandan rundunar Delta Force, yin ritaya a makon da ya gabata.
Wannan gibin shugabanci na faruwa ne a lokacin da Rundunar Sojin Kasa ta Amurka ke fuskantar wasu daga cikin manyan ayyukan soja cikin shekaru, ciki har da yakin da Amurka ke yi da Iran da kuma cigaba da yakin Ukraine.
Lamarin ya sake haifar da tambayoyi kan makomar Rundunar Sojin Kasa ta Amurka da kuma yadda sauye-sauyen da gwamnatin Trump ke yi a manyan mukaman soji za su shafi tafiyar da rundunar da ayyukanta.
