Firaministan Birtaniya Keir Starmer na cigaba da fuskantar matsin lamba daga cikin jam’iyyarsa ta Labour yayin da ake shirin gabatar da jawabin Sarki Charles wanda zai bayyana sababbin dokokin gwamnati na shekara mai zuwa a yau Laraba.
Ana sa ran Starmer zai gana da Sakataren Lafiya Wes Streeting a gidan gwamnati na Downing Street, a wata ganawa da ake gani a matsayin mai muhimmanci saboda rade-radin cewa Streeting na daga cikin masu neman maye gurbin Starmer.
Lamarin na zuwa ne bayan ministoci hudu sun yi murabus a ranar Talata, yayin da sama da ‘yan majalisar Jam’iyyar Labour 80 suka bukaci Firaministan ya sauka daga mukaminsa ko kuma ya bayyana jadawalin lokacin barinsa.
Sai dai duk da matsin lambar, fiye da ‘yan majalisar Labour 100 sun bayyana goyon bayansu ga Starmer tare da gargadin cewa yanzu “ba lokaci ba ne na rikicin shugabanci.”
A jawabinsa ga majalisar ministoci, Starmer ya ce zai cigaba da gudanar da mulkin kasar duk da matsin lambar siyasa da yake fuskanta.
Daya daga cikin ministocin da suka yi murabus, Miatta Fahnbulleh, ta ce jama’a sun kasa amincewa da Starmer, tana mai cewa ya kamata a tsara “sauyin shugabanci cikin tsari.”
A gefe guda kuma, magoya bayan Starmer na ganin ya samu nasarar dakile yunkurin raba shi da kujerarsa da ake zargin yana fitowa daga bangaren Wes Streeting.
Rahotanni sun nuna cewa fargabar rashin tabbas a siyasar kasar zai kara jefa tattalin arzikin Birtaniya cikin matsala, inda kudin bashin gwamnati ya kai kololuwa tun shekarar 2008.
Masana na danganta hakan da rikicin siyasa cikin gwamnatin Labour da kuma tashin farashin mai sakamakon rikicin Iran.
A yau ne kuma King Charles III zai gabatar da Jawabi a majalisa, inda ake sa ran gwamnati za ta bayyana sabbin kudurori sama da 35 da suka hada da dokokin shige da fice, gyaran harkokin lafiya, sauye-sauyen ‘yan sanda da kuma dangantakar Birtaniya da Tarayyar Turai.
Sai dai masu sharhi na ganin rikicin shugabanci da ke addabar gwamnatin Starmer na iya mamaye muhimman manufofin da gwamnati ke son gabatarwa.
