Saurari premier Radio
32.9 C
Kano
Saturday, April 27, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiRundunar yansandan Kano na neman diyyar Naira dubu 500 daga hannun juramar...

Rundunar yansandan Kano na neman diyyar Naira dubu 500 daga hannun juramar Tiktok, Murja Kunya

Date:

Rundunar yansandan Kano ta nemi jarumar nan ta TikTok, Murja Ibrahim Kunya da ta biya ta diyyar Naira dubu dari biyar.

Rundunar ta shigar da wannan bukatar ce a gaban babbar kotun jihar Kano da ke titin Milla, karkashin jagorancin Mai Shari’a Nasiru Saminu.

Rundunar ta ce neman diyyar ya biyo bayan shigar da su kara da jarumar Murja Kunya din ta yi ba tare da sun aikata laifin komai ba, sai dai kawai don ta bata wa shari’a lokaci.

A martanin da ta mayar a gaban kotun, rundunar ta bakin lauyanta Barista Abdussalam Saleh Dan mai daki, ta nemi kotun da ta cire sunanta daga jerin wadanda ake kara saboda ba su da masaniya kan shari’ar.

Mai Shari’a Nasiru Saminu dai ya dage sauraron shari’ar zuwa ranar 25 ga watan Maris din nan domin yanke hukunci.

A makonnin da suka gabata ne dai, Murja Kunya ta shigar da ƙara gaban kotun tana kalubalantar babban lauyan Gwamnatin Kano, da alkalin kotun shari’ar Musulunci ta PRP da kwamishinan yan sandan Kano da hukumar Hisbah da hukumar da ke kula da asibitocin Kano, hadi da asibitin kula da masu lalurar kwakwalwa da ke Dawanau.

Latest stories

Related stories