Saurari premier Radio
36.9 C
Kano
Saturday, April 13, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiRashin biza daga Saudiyya zai hana dubban yan Najeriya zuwa Umara a...

Rashin biza daga Saudiyya zai hana dubban yan Najeriya zuwa Umara a Ramadan

Date:

Dubban maniyyata daga Najeriya na iya rasa Umara a wannan wata na Ramadan saboda matakin da hukumomi kasar Saudiyya suka dauka na dakatar da bayar da bizar Umarar.

Tuni dai mataki ke kara zama barazana ga masu niyyar zuwa Umarar a dai-dai lokacin da aka shiga kwana na 12 da azumin Ramadan.

Har ila yau, kamfanonin dake hada hadar aikin hajji da Umara na iya fuskantar asarar makudan kudade saboda kudaden otal da suka biya birnin Makkah da Madina.

Rahotan Daily Trust ya bayyana cewa tuni aka soke wasu jirage da suka yi niyyar jigilar maniyyatan aikin Umarah.

Wata majiya ta shaida wa jaridar cewa ko a ranar Talata akwai wani jirgi da yayi niyyar tashi daga jihar Kano zuwa kasar Saudiyya dake dauke da mutum sama da 300 amma ya kasa tashi saboda yawancin fasinjojin ba su samu bizarsu ba.

Watan azumin Ramadan ya kasance lokacin al’ummar Musulmi ke yawan zuwa Umarar domin samun halartar kwanaki 10 na karshen azumin a kasar Saudiyya.

Kawo yanzu dai hukumar kula da aikin hajji ta Najeriya NAHCON, ba ta bayyana matakin da take shirin dauka a hukumance ba domin magance wannan matsala.

Latest stories

Gov. Yusuf Clashes with Ganduje over Governance Failure Accusations

Karibu Abdulhamid Kano State Governor, Alhaji Abba Kabir Yusuf, and...

Related stories