Saurari premier Radio
39.7 C
Kano
Friday, April 12, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiGwamnonin Jihohi 16 sun mika rahoton nuna goyon bayansu ga kafa yan...

Gwamnonin Jihohi 16 sun mika rahoton nuna goyon bayansu ga kafa yan sandan jihohi ga majalisar tattalin arziki

Date:

Gwamnonin Jihohi 16 sun mika rahoton nuna goyon bayansu ga kafa yan sandan jihohi ga majalisar tattalin arzikin kasa.

Sun kuma bayar da shawarar yin sauye-sauye ga kundin tsarin mulkin kasa domin bayar da damar kafa yan sandan jihohin.

Gwamnonin sun mika rahoton ne yayin taron majalisar karo na 140 wanda mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya jagoranta a fadar shugaban kasa dake Abuja ranar Alhamis.

Mai bai wa mataimakin shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai Stanley Nkwocha ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya da ya fitar.

A cewar sanarwar, majalisar tattalin arzikin kasar har yanzu tana jiran rahotanni daga jihohi 20,inda ta ke da kwarin gwauwar cewa sauran suma za su goyi baya.

Al’ummar kasar dai na fama da tashe-tashen hankula na sace-sacen jama’a da hare-haren yan bindiga lamarin da ke kara farfado da kiraye-kirayen inganta tsarin aikin yan sanda ciki har da yan sandan jihohi.

Latest stories

Gov. Yusuf Clashes with Ganduje over Governance Failure Accusations

Karibu Abdulhamid Kano State Governor, Alhaji Abba Kabir Yusuf, and...

Related stories