Saurari premier Radio
33.9 C
Kano
Saturday, April 27, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiKudirin bai wa masu takaba hutun watanni biyar ya tsallake karatu...

Kudirin bai wa masu takaba hutun watanni biyar ya tsallake karatu na biyu a majalisar wakilai

Date:

Ɗan majalisa Sa’idu Abdullahi ne ya samar da kudurin don a dinga bai wa matan da zamansu suka rasu isasshen lokacin yin alhini da kuma samun damar shirya wa kalubalen da ke gabansu.

Sa’idu ya ce akwai bukatar yin la’akari da kudurin saboda dalilai na addini da al’ada kuma an tsara wannan kudirin ne domin sanya kasar nan a jerin kasashen da ke kan gaba a fannin walwalar ma’aikata kasancewar akwai dokar a kasashe da dama.

A cewarsa, binciken da aka gudanar ya nuna cewa a kasar nan, hukumomi da ma’aikatun gwamnati kan ba da hutun kwanaki 14 ne kawai ga ma’aikatan da abokan zamansu.
Sai dai ya ce kwanaki 14 sunyi kadan idan aka yi duba da yanayin al’adu da addini al’umma.

Shugaban majalisar, Tajudeen Abbas ya mika kudurin ga Kwamitin Sauye-Sauyen Bangarorin da suka shafi Jama’a don kara nazari.

Wasu addinan sun tanadi tsawon lokacin da ya kamata masu takaba su yi kafin komawa harkokinsu na yau da kullum. Alal misali a Musulunci, ana so mace ta yi takabar rasuwar mijinta har tsawon wata huɗu da kwana 10.

Latest stories

Related stories