Saurari premier Radio
27.2 C
Kano
Saturday, April 27, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiMajalisun tarayya sun amince da dokar bai wa dalibai bashin karatu a...

Majalisun tarayya sun amince da dokar bai wa dalibai bashin karatu a manyan makarantu

Date:

Majalisun tarayya sun amince da dokar bai wa dalibai bashin karatu a manyan makarantun kasar nan, wadda ta sha caccaka a baya.

Wannan dai na a matsayin gyara da kuma sake amincewa da ita, kasancewar a baya yan majalisun sun amince da ita, amma daga bisani aka gano kura-kurai a cikinta.

Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ne ya bijiro da dokar tare da mika wa yan majalisar domin amincewa da ita.

Dokar ta kunshi bai wa dalibai bashin kudade domin biyan kudin makaranta da sauran bukatun yau da kullum da suka shafi karatunsu, inda za su fara biya da zarar sun kammala karatu, sun samu aikin yi ko kuma sun kama sana’a.

Sai dai kuma tun a wancan lokaci kungiyoyin dalibai da na fararen hula suka fara caccakar sabuwar dokar, a ganinsu tamkar bautar da dalibai ne a fakaice, kan maimakon su fara amfani da albashinsu wajen gina rayuwa bayan samun aiki sai su bige da biyan gwamnati bashi.

A maimakon haka kungiyoyin na ganin kamata ya yi gwamnati ta sassauta kudaden makaranta ta yadda kowa zai iya biya da kudinsa ba tare da karbar bashi ba.

Latest stories

Related stories