Tsohon gwamnan Jihar Jigawa kuma jigo a jam’iyyar PDP, Sule Lamido, ya ce ya haƙura da tunanin tsayawa takarar shugaban ƙasa saboda yadda matasa suka nuna ba sa son tsofaffi su jagorance su. Sule Lamido ya ce duk da cewa yana da gogewa da kuma tarihin siyasa da zai ba shi damar neman wannan muƙami, ya fahimci cewa yanayin siyasar yanzu ya sauya, inda matasa ke nuna sha’awar ganin sabbin jini sun jagoranci ƙasar.
Lamido ya ƙara da cewa dole ne shugabannin siyasa su mutunta ra’ayin jama’a tare da fahimtar sauye-sauyen da ke faruwa a tsarin siyasa.
Tsohon gwamnan ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da ya yi da kafar yaɗa labarai ta Explorer Hausa.
