Akalla mutane 1,000 sun rasa matsugunansu sakamakon sabon rikicin kabilanci a Ƙaramar Hukumar Sardauna ta Jihar Taraba.
Rikicin ya kuma yi sanadin konewar gidaje kusan 340, lamarin da ya tilasta wa wasu mazauna yankin tserewa zuwa ƙasar Kamaru da wasu garuruwan da ke makwabtaka da yankin.
Wasu shaidu sun ce an kashe mutane da dama, ciki har da wani jami’in Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS), yayin da wasu kuma ake zargin sun ɓace.
Sai dai har yanzu ba a tabbatar da adadin mutanen da suka mutu ko suka ɓace ba.
Shugaban Ƙaramar Hukumar Sardauna, Alhaji Mohammed Umar, ya tabbatar da faruwar rikicin, yana mai cewa ya samo asali ne daga wata takaddama tsakanin wata mata ’yar Mambilla da wani makiyayi Bafulatani a wata gona.
Ya ce an tura jami’an tsaro yankin domin dawo da zaman lafiya, tare da ɗaukar matakan ganin an dawo da mutanen da suka tsere zuwa Kamaru.
