Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta sun ceto matafiya 49 daga Kano, bayan wasu ‘yan bindiga sun yi yunkurin yin garkuwa da su a jihar Zamfara.
Rahoton jaridar Vanguard ya ce matafiyan suna kan hanyarsu ta komowa Kano ne daga kasar Senegal, inda suka je wajen wani taron Mauludi, lokacin da motarsu ta samu matsala a kan hanya.
Lamarin ya faru ne a wani yanki na jihar Zamfara, inda ake zargin masu garkuwa da mutane sun yi amfani da tsayawar motar wajen kai musu hari.
Dakarun Operation Fansan Yamma sun isa wurin bayan samun rahoton lamarin, inda suka yi artabu da wadanda ake zargin masu garkuwa da mutanen ne.
Rundunar ta ce an samu nasarar ceto dukkan matafiyan 49, sannan aka mika su ga shugaban karamar hukumar Tsafe, Malam Garba Shehu Fanchers.
An kai wadanda aka ceto domin duba lafiyarsu da kula da bukatunsu, yayin da ake shirin mayar da su ga iyalansu.
Rundunar ta ce lamarin ya nuna cigaba da kokarin dakile garkuwa da mutane a yankin Arewa maso Yamma
