Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta dage sauraron wata shari’a da ke kalubalantar shugabancin jam’iyyar ADC zuwa ranar 5 ga Oktoba.
Tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar ADC na ƙasa, Nafiu Bala Gombe, ne ya shigar da ƙarar yana neman kotu ta rushe shugabancin jam’iyyar .
Mai shari’a Peter Lifu Ya umarci bangarorin da su shigar da dukkan takardun da suka shafi shari’ar cikin sa’o’i 48.
Alƙalin ya kuma umarci a aika sanarwar sauraron shari’ar ga Hukumar Zaɓe ta Ƙasa mai zaman kanta (INEC), wadda aka sanya a matsayin wadda ake ƙara ta huɗu.
Nafiu Bala, ya kuma nemi kotu ta hana David Mark, Rauf Aregbesola da mambobin kwamitin gudanarwa na wucin gadi na jam’iyyar bayyana kansu a matsayin shugabannin ADC.
