Hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Yobe (SEMA) ta tabbatar da cewa wasu yara biyu sun nutse a wani kogi da ke garin Dapchi, a ƙaramar hukumar Bursari ta jihar, inda aka gano ɗaya daga cikinsu, yayin da ake ci gaba da neman ɗayan.
Daraktan ayyukan bincike da ceto na hukumar, Dr Muhammad Jalo, ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 2:30 na ranar Lahadi, 4 ga Oktoba, a Unguwar Bulama Ahmadu da ke cikin garin Dapchi.
Ya bayyana cewa jami’an ceto na jiha da ƙaramar hukuma, tare da wasu masu nutso na yankin, sun fara aikin neman yaran nan take bayan samun rahoton faruwar lamarin.
A cewar Jalo, zuwa ƙarfe 5 na yamma, an gano ɗaya daga cikin yaran mai suna Goni Mustapha, mai shekaru 14, yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin gano ɗayan.
Hukumar ta yi kira ga iyaye da masu kula da yara da su riƙa sanya ido a kansu, musamman a wannan lokacin damina da koguna da sauran magudanan ruwa ke cika, tare da ƙara haɗarin nutsewa.
Hukumar ta kuma shawarci mazauna yankunan da ke kusa da koguna da su ƙarfafa matakan kariya, tare da kai rahoton duk wani haɗari ga jami’an ceto cikin gaggawa domin kauce wa asarar rayuka.
