Rahotanni sun bayyana cewa Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya rubuta wa Ministan Ayyuka, David Umahi, wasika inda ya buƙaci gwamnatin tarayya ta soke kwangilar aikin titin Kano-Gwarzo-Dayi bisa zargin rashin gamsasshen aikin da kamfanin da ke gudanar da aikin ke yi.
Aikin titin ya haɗa da faɗaɗa titin mai tsawon kusan kilomita 100 daga hannu ɗaya zuwa biyu, domin sauƙaƙa zirga-zirga da kuma taimaka wa manoma da yan kasuwa wajen jigilar kayayyaki zuwa kasuwanni a jihohin makwabta.
A cewar wata wasika da aka ce ta fito daga ofishin Sanata Barau kuma ta samu karɓuwa a Ma’aikatar Ayyuka ta Tarayya a ranar 8 ga Yunin 2026, ya nuna damuwa kan yadda kamfanin CGC Nigeria Limited, wanda ke aikin, ke tafiyar da kwangilar.
Sanatan ya bayyana cewa duk da dimbin kuɗaɗen da aka ware wa aikin a kasafin kuɗin ƙasa, har yanzu ba a samu ci gaba mai gamsarwa ba.
Ya ce jinkirin kammala aikin na jefa mazauna yankin, matafiya da masu gudanar da harkokin kasuwanci cikin matsaloli, kasancewar titin na da matuƙar muhimmanci ga bunƙasar tattalin arzikin jihohin Kano, Katsina da Kebbi.
A cikin wasikar, Barau ya ce: “Duba da muhimmancin titin Kano-Dayi ga ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al’ummar Kano, Katsina da Kebbi, abin damuwa ne yadda kamfanin ya kasa nuna ci gaba mai gamsarwa duk da ware Naira biliyan 19 a kasafin 2025 da kuma naira biliyan 37 a kasafin 2026 domin aikin.”
Ya ƙara da cewa ci gaba da jinkirin aikin na haddasa wahalhalu ga al’ummar yankin da masu amfani da titin.
Sanatan ya kuma buƙaci Ma’aikatar Ayyuka ta Tarayya da ta gaggauta tantance aikin kamfanin, tare da soke kwangilar idan aka tabbatar ba ya iya cika alƙawuran da ke kansa.
“Saboda ci gaba da jinkirin aikin da kuma gazawar kamfanin wajen cimma matakan da ake buƙata, ina kira ga ma’aikatar da ta yi cikakken nazari kan aikin tare da soke kwangilar domin kare muradun jama’a,” in ji Barau.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, Ministan Ayyuka, David Umahi, da kamfanin CGC Nigeria Limited ba su fitar da wata sanarwa a hukumance kan batun ba.
