Ɗan takarar gwamnan jihar Kano na jam’iyyar NDC kuma tsohon Mataimakin Gwamnan jihar, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, ya kalubalanci gwamnatin Kano da ta gabatar da hujjoji kan zargin cewa ya karɓi kuɗaɗe daga ƙananan hukumomin jihar ta hannun ɗansa, Mujahid Aminu Abdussalam.
Kalubalen na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin Kwamared Gwarzo, Ibrahim Garba Shuaibu, ya fitar a ranar Alhamis, a matsayin martani ga zargin da kakakin Gwamnan Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya yi.
Sanarwar ta ce zargin da ake yi wa tsohon mataimakin gwamnan ba shi da tushe, tare da bayyana shi a matsayin wani yunƙuri na bata masa suna da kuma lalata mutuncin da ya gina a tsawon rayuwarsa ta aikin gwamnati.
A cewar sanarwar, “Waɗannan zarge-zarge ba su da wata hujja kuma hasashe ne kawai. Don haka muna ƙalubalantar masu yin zargin da su gabatar da ingantattun hujjoji da za su tabbatar da iƙirarin nasu.”
Sanarwar ta ƙara da cewa maimaita zarge-zarge a kafafen yaɗa labarai ba ya zama hujja, sai an gabatar da shaidu masu gamsarwa.
Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ya kuma jaddada cewa a duk tsawon lokacin da ya yi yana aiki, ya kasance mai bin ƙa’idodin gaskiya, riƙon amana da mutunta doka.
Ya bayyana ƙwarin gwiwar cewa gaskiya za ta bayyana a ƙarshe, tare da yin kira ga al’umma da su yi watsi da abin da ya kira zarge-zargen marasa tushe.
