Jam’iyyar PRP ta musanta rahotannin da ke cewa ta sayar wa tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, fom 69 na takara, tana mai bayyana zargin a matsayin mara tushe.
Jam’iyyar ta ce tuni mambobinta suka sayi dukkan fom ɗin takararta kuma suka cike su, tana mai jaddada cewa Kwankwaso ba mamba ba ne a cikinta, don haka ba zai iya saye ko mallakar fom ɗin takarar jam’iyyar ba kamar yadda ake yaɗawa.
Da yake zantawa da manema labarai a ranar Litinin, Sakataren PRP na jihar, Musa Maigari, ya ce: “Ya zuwa yanzu, an kammala cike dukkan kujerun takara a jam’iyyar PRP. An gama zaɓen fidda gwani, kuma dukkan jam’iyyun siyasa sun kammala shirye-shiryensu na cikin gida.”
Ya kuma ce mutumin da ya fito da wannan zargi ba shi da wata alaƙa da jam’iyyar.
Maigari ya ƙara da cewa babu wani tarihi ko shaidar wata mu’amala tsakanin PRP da Kwankwaso ko wakilansa dangane da saye ko mallakar fom ɗin takara.
Ya ce lokacin da aka fito da wannan zargi ma ya nuna rashin sahihancinsa, domin jam’iyyar ta riga ta kammala zaɓen fidda gwani kuma ta ci gaba da shirye-shiryenta na gaba.
Sakataren ya buƙaci al’umma su yi watsi da abin da ya kira “jita-jita marasa tushe”, tare da yin kira ga jama’a su riƙa dogaro da bayanan da ke fitowa daga jam’iyyar a hukuman ce.
