Hukumar Kula da Cututtuka da Rigakafi ta Najeriya NCDC ta bayyana cewa mutane akalla 214 sun rasa rayukansu sakamakon cutar zazzabin Lassa a faɗin ƙasar nan tun daga farkon shekarar 2026.
A cewar hukumar, adadin masu kamuwa da cutar ya kai kashi 25 cikin 100, wanda ya fi na shekarar 2025 a irin wannan lokaci.
Rahoton NCDC ya nuna cewa duk da raguwar sababbin masu kamuwa da cutar a wasu makwannin baya-bayan nan, har yanzu cutar na ci gaba da barazana ga lafiyar jama’a a wasu jihohin ƙasar.
Hukumar ta yi kira ga gwamnatocin jihohi da al’umma da su ƙara himma wajen tsafta, adana abinci yadda ya kamata da kuma hana beraye shiga gidaje, kasancewar su ne manyan masu yaɗa cutar.
Lassa cuta ce da ake kamuwa da ita ta hanyar hulɗa da fitsari ko kashin berayen da ke ɗauke da ƙwayar cutar, kuma tana daga cikin cututtukan da ke yawan ɓarkewa a Najeriya musamman a lokacin rani.
