Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta sake kunna wani faifan bidiyon hira da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya yi a gidan talabijin na Arise TV, yayin da lauyan kare hakkin dan Adam, Deji Adeyanju, ya ba da shaida a shari’ar da Hukumar Tsaro ta Farin Kaya DSS ta shigar a kansa kan zargin sauraren wayar wasu jami’an gwamnati.
Adeyanju, wanda ya kasance shaida ta biyu a bangaren masu gabatar da kara, ya shaida wa kotun karkashin jagorancin Mai Shari’a Joyce Abdulmalik cewa bidiyon hirar da aka sake kunnawa ta yi daidai da abinda ya ji da kunnensa a shirin Arise TV na ranar 13 ga Fabrairu.
Ya bayyana cewa kafin wannan rana, an samu rahotannin cewa jami’an tsaro na iya gayyatar ko kama El-Rufai bayan dawowarsa daga birnin Alkahira na ƙasar Masar.
A cewarsa, ya yi kira ga tsohon gwamnan da ya amsa duk wata gayyata daga jami’an tsaro, yana mai cewa bai dauki lamarin a matsayin siyasa ba.
Adeyanju ya ce shi ma ya halarci wannan shirin na Arise TV, sai dai nasa bangaren ya biyo bayan na El-Rufai.
Bayan bukatar lauyoyin gwamnati, kotun ta sake kunna bidiyon hirar da aka gabatar tun da farko a matsayin hujja.
Bayan kallon bidiyon, Adeyanju ya tabbatar da cewa abin da ke cikin bidiyon shi ne ya gani a ranar da aka yi hirar.
A yayin tambayoyin da lauyan El-Rufai, Paul Erokoro SAN, ya yi masa, an tambaye shi ko ya ji El-Rufai yana cewa kai tsaye ya saurari ko ya kutsa cikin wata waya.
Adeyanju ya amsa da cewa El-Rufai ya ce: “Mun saurari kiran wayoyinsu.”
Sai dai ya ce bai san yadda aka yi hakan ba, kuma idan wani ya ce an kutsa cikin wayarsa, zai kai rahoto ga hukumomi.
Daga bisani, Mai Shari’a Joyce Abdulmalik ta dage sauraron karar zuwa ranar 23 ga Yuni domin ci gaba da shari’ar.
DSS ta gurfanar da El-Rufai a watan Fabrairu kan tuhume-tuhume guda biyar bayan ya yi ikirari a wata hira da Arise TV cewa ya samu bayanan wata tattaunawar waya da ta shafi Mai Bai Wa Shugaban Kasa Shawara Kan Tsaro, Nuhu Ribadu, wadda a cewarsa ta nuna akwai shirin kama shi.
An gurfanar da El-Rufai a gaban kotu a ranar 23 ga Afrilu, inda ya musanta dukkan zarge-zargen da ake masa, sannan kotu ta ba shi beli kan kudi naira miliyan 100.
