Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya amince da yin karin girman ga ma’aikatan hukumar Ilimin bai-daya ta Jihar SUBEB, guda 18,984, wadanda suka cancanci karin girman na watan Janairu da Yuli 2026.
Amincewar ta biyo bayan bukatar da Shugaban SUBEB, Yusuf Kabir, ya gabatar ga gwamnati, inda ya nemi sakin sama da Naira miliyan 235.1 domin aiwatar da karin girman a ma’aikatun ilimin kananan hukumomi 44 na jihar.
SUBEB ta ce ma’aikatan da abin ya shafa sun hada da malamai, ma’aikatan da ba malamai ba, wadanda aka kammala tantance cancantarsu tare da lissafin karin albashin da ya kamata su samu sakamakon karin girman.
Hukumar ta bayyana cewa gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta kuma samu nasarar magance basussukan karin girman ma’aikata da gwamnatin da ta gabata ta bari, ciki har da wadanda suka shafe shekaru bakwai, lamarin da ta ce ya karawa ma’aikata kwarin gwiwa.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito hukumar ta SUBEB na cewa tana da kusan ma’aikata 60,000 waɗanda da ke aiki a fadin ma’aikatun ilimin kananan hukumomi 44, inda ta jaddada cewa aiwatar da karin girman zai taimaka wajen kara karsashin ma’aikata da inganta ayyukan ilimin bai-daya a jihar.
