Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya ayyana zaman makoki na ƙasa tsawon kwana uku domin girmama mutanen da suka rasa rayukansu a hatsarin jirgin sama da ya faru a Jihar Ondo jiya Litinin.
Shugaban ya kuma bayar da umarnin cewa a sauke tutocin Najeriya zuwa rabin sandar tuta a faɗin ƙasar, domin nuna girmamawa ga waɗanda hatsarin ya rutsa da su.
Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Yaɗa Labarai Bayo Onanuga ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a daren jiya Litinin.
Tun da farko, Shugaba Tinubu ya bayyana alhininsa game da hatsarin jirgin saman na rundunar sojin sama.
Hatsarin ya faru ne a kusa da wani sansanin sojojin ruwa da ke yankin Igbokoda a Jihar Ondo.
Jirgin, wanda ke ɗauke da fasinjoji 25 da ma’aikatan jirgin guda bakwai, yana kan bakin aikin sa ne daga Benin zuwa Legas.
A cikin saƙon ta’aziyyar da Fadar Shugaban Ƙasa ta fitar zuwa ga Shugaban Rundunar Sojin Sama, Air Marshal Sunday Kelvin Aneke, da dukkan jami’ai da sojoji maza da mata na Rundunar Sojin Sama ta Najeriya, Shugaba Tinubu ya ce “Wannan lokaci ne mai matuƙar raɗaɗi ga Rundunar Soji da kuma al’ummar ƙasar baki ɗaya.
Ya kuma yaba wa Rundunar Sojin Sama bisa gaggauta fara aikin bincike da ceto bayan faruwar hatsarin.
