Matasan jam’iyyar ADC sun kai ƙarar alkalin Babbar Kotun Tarayya Mai Shari’a Peter Lifu gaban Hukumar Kula da Harkokin Shari’a ta Kasa (NJC), domin binciki yadda ya alkalin ya hukuncin soke rajistar jam’iyyar ADC da wasu jam’iyyu huɗu.
Sai dai matasan ADC sun ce hukuncin ya saɓa wa umarnin Kotun Ɗaukaka Ƙara da ta dakatar da ci gaba da sauraron shari’ar tun kafin a yanke hukunci.
A cikin koken da suka miƙa wa NJC, wanda shugaban matasan ADC na ƙasa, Balarabe Rufai, ya sanya wa hannu, sun nemi a cire Mai Shari’a Peter Lifu daga duk wasu shari’un da suka shafi jam’iyyar.
Da yake magana da manema labarai a hedikwatar ADC da ke Abuja, wakilin shugaban matasan jam’iyyar, Ibrahim Wala, ya yi zargin cewa jami’an tsaro sun hana su kai koken zuwa ofishin NJC, inda ya ce an toshe hanyoyin da ke kaiwa harabar hukumar da jami’an tsaro masu ɗauke da makamai.
Matasan sun yi kira ga NJC da ta binciki alkalin tare da ɗaukar matakan ladabtarwa idan an same shi da laifi, suna masu cewa za su ci gaba da fafutuka har sai an magance korafinsu.
A ranar Litinin ne Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ƙarƙashin Mai Shari’a Peter Lifu, ta umarci Hukumar Zaɓe ta Kasa (INEC) da ta cire ADC, Action Peoples Party (APP), Action Alliance (AA), Accord Party (AP) da Zenith Labour Party (ZLP) daga rijistar jam’iyyun siyasa bisa zargin rashin cika wasu sharuddan doka.
