Saurari premier Radio
35.9 C
Kano
Friday, June 14, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiMajalisar Wakilai Ta Amince A Dawo Da Tsohon Taken Najeriya.

Majalisar Wakilai Ta Amince A Dawo Da Tsohon Taken Najeriya.

Date:

Majalisar Wakilai ta amince da kudirin cigaba da amfani da tsohon taken kasar nan mai suna “Nigeria, We Heil You”.

An maye gurbin tsohon taken na “Nigeria, We Heil You” da na yanzu “arise O Compatriots” a shekarar 1978.

An yi saurin zartar da kudurin dawo da tsohon taken karatu na farko zuwa na uku a cikin mintuna kadan a zauren majalisar wakilan bayan an tafka muhawara.

Shugaban majalisar, Farfesa Julius Ihonvbere, ya yi nuni da bukatar ‘yan Najeriya su dauki taken a matsayin alama ta hadin kan kasa.

Sai dai shugaban marasa rinjaye, Kingsley Chinda, ya yi adawa da kudirin, yana mai cewa tsohuwar wakar tana da alamar mulkin mallaka wanda shi ne dalilin sabunta ta tun a wannan lokacin.

Mista Chinda ya nuna shakku kan mahimmancin sauya wakar a daidai lokacin da ake fuskantar kalubale a kasar.

Sai dai, an gaggauta amincewa da kudirin dokar. A majalisar dattijai, kudirin ya kai matakin karatu na daya da na biyu.

An mika shi ga kwamitin majalisar dattawa mai kula da harkokin shari’a da ‘yancin dan Adam domin yin duba akansa ya kuma gabatar da rahotonsa ga majalisar nan da makonni biyu.

Sanatocin, wadanda suka bayyana baki daya suna goyon bayan kudurin, sun yi nuni da cewa,dawo da tsohon taken Najeriyar zaifi samar da kyakkyawar alama ta hadin kai da zaman lafiya idan aka kwatanta taken na yanzu.

Latest stories

Related stories