Saurari premier Radio
23.5 C
Kano
Tuesday, July 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiGwamnan Jihar Ribas Ya Fitar Da Sakon Taya Murna Sake Dawo Da...

Gwamnan Jihar Ribas Ya Fitar Da Sakon Taya Murna Sake Dawo Da Sarkin Muhammad Sanusi II.

Date:

Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara, ya fitar da sakon taya mai martaba Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II murnar sake dawo da shi kan karagar sarautar Kano.

Gwamna Fubara ya ce yayi farin ciki da samun labarin mayar da tsohon Gwamnan babban bankin ƙasa CBN kan mukaminsa na Sarkin Kano a daidai lokacin da Khalifa Sanusi II, ya je jihar domin bada bayanai da kara kaimi ga yunkurin gwamnatinsa na sake yanayin tattalin arziki.

Ya kara da cewa mayar da Sarki Sunusi kan karagar mulki da gwamnatin jihar Kano ta yi a wannan lokaci ya nuna cewa tsige Muhammadu Sanusi II daga a ranar 9 ga watan Maris na shekarar 2020, ya sabawa abinda alummar Kano ke bukata.

Fabura ya ce mulkin Sarki Sunusi II yayin da yake kan karagar mulki mai daraja da kima, tare da yabawa gwamnatin jihar Kano bisa yadda ta saurari bukatun aluma, da kuma yin aikin gyara kura-kuran da aka yi a baya.

Daga bisani gwamnan na jihar Rivers ya bukaci alummar Kano da su baiwa Sarkin Kano goyon baya domin samun nasara.

Ya kuma bukaci shugaban darikar tijjaniyya ta Najeriya wato sarki Muhammad Sanusi na biyu da ya jagoranci mabiya darikar sufaye sama da miliyan 50 a Najeriya cikin kauna da hikima da jajircewa tare da samar da dawwamammen zaman lafiya da adalci da daidaito da adalci ga kowa da kowa.

Latest stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...

Related stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...