Saurari premier Radio
29.9 C
Kano
Saturday, June 15, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiAn zabi mace ta farko da za ta shugabanci yan majalisun kungiyar...

An zabi mace ta farko da za ta shugabanci yan majalisun kungiyar ECOWAS

Date:

An zabi Maimunatu Ibrahim daga kasar Togo, a matsayin mace ta farko da za ta shugabanci yan majalisun kungiyar kasashen Africa ta yamma ECOWAS.

An yi wannan zabe ne a ranar Alhamis da ke zama rana ta uku da fara gudanar da taron kungiyar a jihar Kano.

Zaben nata ya biyo bayan janye takara da ragowar yan takara guda biyu suka yi wadanda suka fito daga kasar ta Togo.

Da take jawabi bayan karbar ragamar kungiyar, Maimunatu Ibrahim, ta ce shugabancintzai mayar da hankali kan matsalar tsarotattalin arziki da tabbatuwar damokradiyya a yankin Africa ta yamma da samar da kyakkyawan yanayin da zai dawo da kasahsen Nijar, Burkina Faso da Mali cikin ECOWAS.

A nasa jawabin mataimakin shugaban kungiyar Barau I Jibril, wanda kuma shi ne ya yi rikon kwaryar shugabancin kungiyarya ce tafiyar da lamuran kungiyar abu ne da zai kawo karshen matsaloli da yawa a nahiyar Africa, inda ya tabbatar da yin abinda ya dace a tsawon lokacin da za su dauka suna jagoranci.

Da take karin bayani kan abinda zaman majalisar ya kunsa, yar majalisa mai wakiltar Bama, Ngala da Kalabalge dake jihar Borno a majalisar wakilan NajeriyaDr. Zainab Gimba, ta ce suna da babban fata kan sabuwar shugabar tasu.

Yan majalisu 112 ne dai da suka fito daga kasashen yammacin Africa ta yamma suka amince da shugabancin na Maimunatu Ibrahim.

Latest stories

Related stories