Saurari premier Radio
28.9 C
Kano
Monday, May 20, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiMai Wake da Wakili:Takaddama ta kaure kan batun ayyukan raya kasa a...

Mai Wake da Wakili:Takaddama ta kaure kan batun ayyukan raya kasa a Ungogo da Munjibir

Date:

Takaddama ta kaure tsakanin tsohon dan majalisar Ungogo da Munjiburi Sani Ma’aruf mai Wake da kuma mai ci yanzu Sani Adamu Wakili kan ayyukan ci gaban yankin, musamman wadanda aka yi kasafinsu tun 2022/2023.

Ko a ranar 11/1/2024  Mai Wake ya kaddamar da aikin titi a unguwar Bachirawa zuwa katsinawa, a matsayin ragowar aikace-aikacen da ya yi alkawari kafin ya bar mulki.

To sai dai a ranar 21/1/ 2024 shima dan majalisar tarayyar na yanzu, Sani Adamu wakili shima ya kaddamar da aikin kuma ya bayyana cewar shi ne ya nemo aikin.

Wannan ne ya sanya jama’ar mai waken ke zargin dan majalisa mai ci da yin ruf da ciki kan ayyukan tsohon dan majalisar.

A yanzu haka ma ana rade-radin  Sani Wakili zai rabar da wasu motoci, da mabiya mai waken ke cewa  tun a shekarar da ta gabata Mai Wake ya ce akwai motocin hukumar ilimi na kananun hukumomin biyu da kuma na jami’an sintiri, da na hakimai da kuma na daukar gawa wadanda mai Waken ya yi ikirarin samosu

Hakan ce ma ta sanya jama’ar yankin kan ke cewa wannan motoci da ake, rade-radin rabawa wadancan ne da mai waken ya ke bishara da har yanzu ragowar ayyukansa ne suke zuwa.

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...