
Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba zai yi nasara a zaben 2027 ba, da hakan zai ba shi damar komawa mulkin kasar nan.
El–Rufa’i ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a sharin Talbijin na Arise News, a ranar Litinin.
Tsohon shugaban, yana mai cewa raunin tattalin arziki da tabarbarewar tsaro sun jefa Najeriya cikin halin kaka-ni-kayi, don haka goyon bayan jama’a ga gwamnatin APC ya ragu matuka, har ma a yankunan da ake ganin Tinubu na da karfi kamar Ondo da Ekiti.
“Ko a jihohin Kudu maso Yamma, Tinubu bai samu kuri’u fiye da kashi 50 cikin 100 na goyon baya.”
El-Rufai, wanda ya kasance cikin manyan jiga-jigan da suka mara wa Tinubu baya a zaben 2023, ya bayyana nadamar goyon bayan da ya bai wa shugaban kasa, yana mai cewa ya yi tsammanin gwamnatin Tinubu za ta fi ta Buhari sauyi da inganci, amma hakan bai faru ba.