Saurari premier Radio
32.9 C
Kano
Friday, June 14, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiKwamitin haɗin gwiwa na majalisar wakilai ya baiwa kamfanonin ciminti wa'adin kwanaki...

Kwamitin haɗin gwiwa na majalisar wakilai ya baiwa kamfanonin ciminti wa’adin kwanaki 14 su gurfana a gabansu.

Date:

Kwamitin hadin gwiwa na majalisar wakilai, ya bai wa kamfanonin siminti na Dangote Cement da BUA da IBETO da sauransu, wa’adin kwanaki 14 su gurfana a gabansa domin amsa tambayoyi kan tsadar siminti a kasar nan.

Hakan ya biyo bayan gazawar da kamfanonin suka yi wajen halartar zaman ganawa da kwamitin ya gudanar a Talatar nan.

Kwamitin hadin gwiwar wanda ya kunshi kwamitocin majalisar, masu kula da ma’adanai da kasuwanci da masana’antu da ayyuka na musamman, majalisar ta kafa shi ne domin binciken karin farashin siminti a kasar nan da kamfanonin suka yi.

Majalisar ta kuma gayyaci ministan ma’adanai, Dele Alake, da ya gurfana a gaban kwamitin a Talatar makon gobe, bayan ya kasa bayyana a Talatar nan.

Ta kuma bayar da umarnin cewa kamfanin simintin Dangote da BUA da IBETO da sauransu, su bayyana a ranar Litinin mai zuwa.

Shugaban kwamatin na haɗin gwiwa wanda kuma shi ne shugaban kwamitin kula da ma’adanai, dan majalisa Jonathan Gaza Gefwi, ya yi tir da yadda kamfanonin suka yi watsi da gayyatar da aka yi musu, yana mai cewa abin da suka yi na nuni ne da rashin sanin halin da yan kasa ke ciki.

A jawabinsa na buɗe taron tun da farko, Gefwi ya bayyana cewa, bitar farashin siminti a wasu ƙasashe kamar Kenya, Indiya da Zambia a shekarar 2021 kaɗai ya nuna cewa kasar nan ce ta fi kowacce ƙasa farashin siminti.

Latest stories

Related stories