Saurari premier Radio
32.9 C
Kano
Friday, June 14, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiKungiyar lauyoyi ta kasa ta yabawa gwamnan Kano kan sallamar jami'an da...

Kungiyar lauyoyi ta kasa ta yabawa gwamnan Kano kan sallamar jami’an da sukayi kalaman tunzuri

Date:

Kungiyar lauyoyi ta kasa ta yabawa gwamnan Kano kan sallamar jami’an da sukayi kalaman tunzuri.

A daren Juma’a ne gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya sanar da dakatar da wasu mukarrabansa biyu, sakamakon wasu kalamai da suka furta.

Gwamnatin Kano dai ta nesanta kanta daga waɗannan kalamai na kwamishinan kasa da safayo Adamu Aliyu Kibiya da kuma mai baiwa gwamnan Kano shawara kan wasanni da matasa Yusuf Imamu Ogan Boye.

Shugaban kungiyar lauyoyin na Kano, Barr. Suleiman Gezawa ya yabawa gwamnan kan matakin sallamar mukarrabansa biyu.

Yace hakan ya tabbaatar da cewa gwamnan a shirye yake wajen ganin an kawar da duk wata barazana da zata iya kawo cikas ga bangaren shari’a dama zaman lafiyar jihar Kano baki daya.

Latest stories

Related stories