Kotun sauraren kararrakin zabe dake zamanta a Kano ta tabbatar da Mudassir Zawaciki na jam’iyyar NNPP a matsayin wakilin mazabar Kumbotso a majalisar dokokin jihar.
Da yake bayyana hukuncin da kotun ta yanke a yau Litinin, Mai Shari’a L.B Owolabi ya kori karar da Sagir AbdulKadir Panshekara na jamiyyar APC ya shigar yana kalubantar nasarar Zawaciki.
Mai shari’ar ya ce wanda yake karar ya gaza gamsar da kotu cewa an samu aringizon kuri’a, da tashin hankali da kuma bayar da takaddar shaidar karatu ta bogi.
Saboda wadannan dalilai, mai shari’ar ya bayyana cewa kotu ta yi watsi da karar, wanda hakan ke tabbatarwa Mudassir Zawaciki kujerarsa.
