Saurari premier Radio
23.5 C
Kano
Tuesday, July 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin KanoGwamnatin Kano ta rabawa mata a kananan hukumomin TudunWada, Doguwa da Bebeji...

Gwamnatin Kano ta rabawa mata a kananan hukumomin TudunWada, Doguwa da Bebeji raguna da awaki domin bunkasa tattalin arzikinsu.

Date:

Gwamnatin Kano ta rabawa mata a kananan hukumomin TudunWada, Doguwa da Bebeji raguna da awaki domin bunkasa tattalin arzikinsu.
Jami’in Sadarawa na shirin Bunkasa noma da kiwo, Aminu Yassar ya shaidawa Premier radio cewa rabon awaki da ragunan wani mataki ne na rage talauci tsakanin matan jihar Kano.
Ya ce matan da aka rabawa raguna an hada musu da abincin dabbobin na watanni uku, amma wadanda aka bawa awaki ba a basu abincin dambobin ba saboda saukin ciyar da su.

Jami’in Sadarawa na shirin ya kara da cewa duk da yanzu aka fara shirin, ana sa ran mata a dukkan kananan hukumomin dake Kano za su iya samun wannan tallafi nan gaba kadan.

Ya ce shirin raba tallafin awaki da ragunan, yana da tsare-tsaren da gwamnatin Kano ta bijiro da shi wajen ganin mata sun rungumi sana’ar kiwo.

Latest stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...

Related stories