Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yi watsi da karar da aka shigar domin hana tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2027.
Mai shari’a Peter Lifu ya ce kotunan da suka gabata sun riga sun yanke hukunci kan cancantar Jonathan na sake neman shugabanci, saboda haka babu wani sabon dalili da zai hana shi shiga takara.
Kotun ta bayyana karar a matsayin mara tushe, tare da ci wa wanda ya shigar da ita tarar naira miliyan 20.
Lauyan Jonathan, Chris Uche (SAN), ya shaida wa kotun cewa batun ya riga ya samu hukunci tun a kotun tarayya da ke Yenagoa da kuma Kotun Daukaka Kara, yana mai cewa sake dawo da shari’ar “bata lokaci ne kawai.”
A karar mai lamba FHC/ABJ/CS/2102/2025, wani lauya mai zaman kansa daga Abuja, Johnmary Jideobi, ya bukaci kotu ta hana Jonathan gabatar da kansa ga kowace jam’iyya domin neman tikitin takarar shugaban kasa a 2027.
Har ila yau, ya roki kotun ta hana INEC karbar ko wallafa sunan Jonathan a matsayin dan takara.
An hangi jami’an INEC a kotun yayin yanke hukuncin.
Shari’ar na zuwa ne yayin da ake ci gaba da rade-radin yiwuwar dawowar Jonathan cikin siyasa domin sake neman shugaban kasa.
A baya-bayan nan, Jonathan ya bayyana wa wasu matasa da suka bukace shi ya tsaya takara cewa batun neman shugabancin kasa “ba wasan kwamfuta ba ne.”
A gefe guda kuma, jam’iyyar PDP ta bai wa Jonathan tikitin takara kai tsaye tare da cire shi daga tsarin tantance ‘yan takara.
Tsohon gwamnan jihar Neja, Babangida Aliyu, wanda ya yi magana a madadin kwamitin jam’iyyar, ya ce an yi wa Jonathan “rangwame na musamman” wanda ya tabbatar da shi a matsayin dan takarar PDP a zaben shugaban kasa na 2027.
