Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa INEC ta bayyana cewa mutane 1,565,873 sun kammala rajistar katin zaɓe na dindindin (PVC) zuwa ranar 26 ga watan Yuni, a ƙarshen mako na bakwai na zagaye na uku na shirin Ci Gaba da Rajistar Masu Zaɓe (CVR).
Alƙaluman da hukumar ta fitar a ranar Talata a Abuja sun nuna cewa mutane 620,933 sun kammala rajistar farko ta internet, yayin da 944,940 suka yi rajista a cibiyoyin rajista na zahiri.
Sai dai INEC ta bayyana cewa waɗannan alkaluma na wucin gadi ne, domin za a tantance bayanan tare da cire waɗanda suka yi rajista fiye da sau ɗaya ko kuma bayanan da ba su cika ƙa’ida ba.
Bayan haka ne za a yi amfani da tsarin tantance bayanan yatsu da sauran bayanai na (Automated Biometric Identification System – ABIS).
Bayanan sun nuna cewa Jihar Kano ce ta kasance a kan gaba wajen yawan masu rajista, inda mutane 118,207 suka yi rajista, adadin da ya kai kashi 7.55 cikin ɗari na jimillar masu rajista a faɗin Najeriya.
Jihar Legas ce ta zo ta biyu da mutane 78,360 (kashi 5 cikin ɗari), sai Jihar Delta da mutane 76,395, wanda ya kai kashi 4.88 cikin ɗari.
Hukumar ta kuma bayyana cewa an dakatar da rajistar masu zaɓe na ɗan lokaci a jihohin Ekiti da Osun, sakamakon zaɓen gwamna da aka kammala da kuma wanda ke tafe, domin bin tanadin Sashe na 9 (6) na Dokar Zaɓe ta 2022.
Dangane da jinsi, mata sun fi maza yawan rajista, inda mata 821,276 suka yi rajista, adadin da ya kai kashi 52.45 cikin ɗari, yayin da maza suka kai 744,597, wato kashi 47.55 cikin ɗari.
Bayanan sun kuma nuna cewa matasa masu shekaru tsakanin 18 zuwa 34 su ne suka fi yawan yin rajista, inda suka kai 1,082,985, wanda ya yi daidai da kashi 69.16 cikin ɗari na jimillar masu rajista. Masu shekaru tsakanin 35 zuwa 49 sun biyo baya da 331,376, wato kashi 21.16 cikin ɗari, yayin da tsofaffi suka kasance sauran adadin.
Hukumar ta kuma bayyana cewa mutane 18,919 masu nakasa sun samu damar yin rajista a wannan lokaci.
A ƙarshe, INEC ta buƙaci duk waɗanda suka cancanci yin rajistar katin zaɓe amma har yanzu ba su yi ba, da su yi amfani da shafin rajista na internet ko kuma su je cibiyoyin rajista da aka tanada a faɗin ƙasar domin samun damar kaɗa ƙuri’arsu a zaɓukan da ke tafe.
